Insane
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin da biyar


Sayyed Zakzaky2

Ina hukuncin Co-operative Society?
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Allah ya gafarta Malam, menene hukuncin dukiyar da asasinta haramun ne, aka yi tijara da ita ta hanyar halal ta hayayyafa?

Daga Muhammad Abba msabam05@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: Da yake shi ya ce haramun ne, bai fadi yadda ta haramta din ba, wato tana iya haramta a kasantuwar dukiyar wani ce. Kuma wannan yana nufin kenan in aka yi ciniki da ita, da ita da riba din duk kayan mai dukiyar ne. Saboda haka sai a mayar masa da kayansa har da riba din. Kuma idan da faduwa, shi wanda ya yi cinikin shi zai dauki faduwar, amma in ya ci riba, ribar tana ga mai dukiyar ne, kuma ya haramta masa duk wani tasarrufi a kayan da ba nasa ba. Sai mayarwa da mai hakki hakkinsa.


TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halasta ga musulmi ya rika karanta Alkur'ani da addu'o'i ma'asurai kamar su Du'a'u Khumail a zaune a kan kujera ko kishigide?

Daga Muhammad Sani Keffi jihar Nassarawa. muhammasan@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: Akwai ladubba na karatun Alkur'ani da kuma ma na yin addu'o'i. Daga cikin ladubba din akwai tsarki na alwala kenan da fuskantar Alkibla da tara hankali ga abin da mutum yake yi, maimakon yana yi yana shagalta da wadansu abubuwa, ko kuma yana yankewa yana wadansu abubuwa. Har in ya zama tilas ya yanke ya yi wani abu, kamar ya yi magana da wani, to ya kamata ya sa alama ya yanke ya yi wannan abin, a ga cewa lallai ba yana kamar zaman wannan aikin addu'a ko karatun Alkur'ani ba, in ya kammala ya zo ya cika. Ko kuma in wani aiki ne tilas ya yi, sai ya aikata wannan aikin ya dawo kuma ya ci gaba. Wato dai yana da kyau ya lizimci ladubba, wadanda suka hada tsarki da natsuwa da fuskantar Alkibla. Kodayake ba a ce wadannan lalai bane. Saboda haka idan ya zamana mutum cikin wadansu halulluka ya yi addu'a da karatun Alkur'ani, in dai da natsuwa a ciki, babu laifi da shi.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, su waye bai halatta su yi limanci ba?

Daga Mustafa Y. Ibrahim. mustyibrahim@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: To sai ya karanta babin limanci, don wannan yana da tsawo. Akwai sharudda na limanci ga limancin salla kamar Juma'a. Akwai kuma na sauran salloli koma bayan Juma'a, sauran hamsu salawat. Amma da yake tambayar ta cika dunkuluwa, abin da ya fi alheri kawai ya karanta babin limanci zai ga sharudda din a shimfide.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Akramakallah, ya halatta dan Yayar mutum ya ga matarsa ba hijabi?

Daga Yusif A.A.Maigado Kano yusifkurna@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: Wadanda aka lissafta za su ga mace ba hijabi, wato in ta sa kayan yau da kullum, mutane ne da ba zai halatta su aure ta ba ta kowane hali. Shi kuwa dan yayarka yana iya auren matarka in dai ba ta haramta masa ta wata fuska ne ba. Amma dai kasantuwar kai ka auri mace, ba ta haramta ma dan dan uwanka ba, dan uwan naka ma ba ta haramta masa ba ballantana dansa. Saboda haka dole ne ta yi masa hijabi.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam da yake idan zan yi Zuhuraini bayan na yi azan sai na yi ikama, to idan zan yi la'asar sai na yi ikama ne, ko kuwa wacce na yi ta farko ma ta wadatar?

Daga Sani Karami Badawa Kano 0802 791 9966

SHAIKH ZAKZAKY: Idan mutum zai yi sallar azuhur, zai yi azan da ikama. To idan ya sami fasil, rabawa tsakanin azuhur din da la'asar, zai sake maimaita azan da ikama. Wato rabawa din kamar a ce ya yi nafiloli masalan ko kuma ya tashi ya fita ya dawo, in da wani abin da ya raba tsakani. Amma idan da yin azuhur din ne sai ya kabbara la'asar, to ikama kawai zai yi. Idan ba abin da ya raba kenan. Wato kenan idan a gwame aka yi su, azan daya ya wadatar, amma kowacce za ayi mata ikama. Amma in an raba su, kowacce za a yi mata azan da ikamanta. Rabawar kuma yana iya zama in nafila ta shiga tsakani ko kuma an sami dan tazarar lokaci ko kuma ya shagalta da wani aiki na wani abu ba sallar ba sannan ya zo ya ci gaba da salla.

TAMBAYA: Assalamu alikum. Ni ina aiki ne a Karamar Hukuma, kuma ga shi ba ni da wata sana'a, sai aka ce za a ba mu rancen kudi a banki domin yin sana'a, za mu iya karba kuwa?

Daga Abdullahi Giyade jihar Bauci

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, za ku iya karbar rance daga banki, ba wata mishkila. Musamman lasiman kamar siffar da ya nuna cewa kamar shi mabukaci ne ga yin wannan, ganin cewa albashinsa kila bai ishe shi ba sai ya hada da wani abu.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ina hukuncin Co-operative society da kuma daukar bashin da suke rabawa a karshen shekara?

Daga Umar Murtala 0802 727 4921

SHAIKH ZAKZAKY: Wannan babu laifi da shi tunda abin da Co-operative society yake nufi, shi ne su masu sayen kaya ne, sukan harhadu su sayi kaya kamar na sari, amma su saya a tsakaninsu da farashi mai rahusa, ka ga sun tsallake mai sayen sari ya zo ya sai da ma masu saye su yi amfani da shi kenan, kamar tsallake shi suka yi. Maimakon ribar nan da mai sari kan ci, su sai su same shi a saukin kaya. Wannan shi ne abin da Co-operative yake nufi. Kuma bashin da suke badawa ma kamar dai bashi ne wanda mutumn zai ba ka, ba maraba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Akramakallah, muna cikin tafiya a cikin tawaga ne daga garin da nake aiki, wato Abuja zuwa Yola, sai muka ya da zango a Mahaifata, wato Bauci don sallatar Zuhuraini. To, Malam tunda ni zan cika salla ne, yaya zan yi da nafiloli, ko albarkacin muna cikin tafiya nafilolin sun fadi a kaina?

Daga Adamu Madi Ganki Labo 0802 910 6943

SHAIKH ZAKZAKY: Na farko dai ban san ko ma dai cika sallar zai yi ba. Domin kasantuwar Bauci mahaifarsa ne, ba lalai ne ya zama zai cika salla ba. Tana iya yiwuwa yanzu ya tashi a mutumin Bauci ya zama mutumin Yola. Saboda haka Baucin ya zama ba gidansa ba, ko da kuwa an haife shi ne a wurin. Ana cewa ko da an haife ka a wuri, idan yanzu ka daina ganin sa a matsayin gidanka, za ka yi kasaru ne. Saboda haka tana iya yiwuwa ma zai iya yin kasaru.

Amma ala ayyi halin idan cika salla ya zo, ya zama zai cika salla ne, shi kenan hukuncinsa ya zama na mazauni. Saboda haka har walayau sai ya yi nafilolinsa.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Nine na tafi aikin Hajji, sai ya zamo na yi hadaya kafin Arfah. Shin yaya matsayin wannan hadayar da na yi kenan?

Daga Abdul'aziz Salisu Dagacin U/ Ma'azu Kaduna 0803 258 5682

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba ka yi hadaya ba. Saboda haka ka dai yanka abin yankawa kuma an ci nama, amma hadaya na nan a kanka. Sai ka aika da abin hadaya din ga wadanda za su je wani Hajji mai zuwa in kai ba ka koma ba, su yi maka hadaya din. Ko kuma in ka koma kai ka sake yin wancan hadayar da ka yi, domin lallai ba ka yi hadaya ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum ne yake da kafa biyu, sai lalura ta same shi ya zama ba shi da daya kafar, a madadinta sai aka yi masa ta katako. Yaya zai yi wajen alwala kenan? Zai yi shafa kan gundulmin ne? Ko kuma a kan wannan katakon zai yi?

Daga Abdul'aziz Salisu Dagacin U/ Ma'azu Kaduna 0803 258 5682

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai in da ragowar kafar, abin da ya yi saura na kafar zai shafa, in kuma ba ma kafar sam-sam, tsawon inda aka yanke ya wuce gabar da ake shafa samsam har ya je kamar misali cinya, to shi kenan sai ya manta da shafa din, bai hau kansa ba tunda ba shi da muhallin shafa din. Amma in da kwabri, kamar can wajen karshen kwabri, yana iya shafar abin da ya yi saura ko yaya. Amma ala ayyi halin ba zai shafi katako ba saboda ba kafa ne ba.

TAMBAYA: Malam ina neman a yi min karin bayani game da muryar mace a wajen waka da aka ce haramun ce. To Malam idan mace tana miji ya halatta su yi waka tare, misali wajen tallace-tallace?

Daga Muhadammad Sani mohsanhas@saudia.com

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da aka ce shi ne ita muryar mace din ne kadai, ta karya shi da sigar waka ya haramta Ajanabi ya ji. Amma muryar tata a cikin mutane masu yawa, ko da duk cikarsu mata ne, to shi kenan wannan babu komai da shi. Saboda haka idan mata suka yi waka da murya daya, to ba laifi da wannan.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ya halascin amfani da man 'relaxer' da mata kan yi 'famin' da shi wajen gyaran gashinsu?

Daga Fatima Bashir Abuja

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ban san wannan mai din ba wanda ya kira shi 'Relaxer.' Ko ma menene dai, mutum ba zai yi amfani da abin da yake najasa ba. Saboda haka idan mai din yana da tsarki, ya halatta ta yi amfani da shi wajen sawa a gashi ne ko jiki.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din